Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Gamduje ya ce babu batun siyasantar da tsarin mayar da almajirai jihohinsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake yiwa manema labarai jawabi kan annobar cutar mashaƙon numfashi ta Covid 19.

Ya ce ba abin surutu bane ganin yadda ake mayar da almajirai jihohinsu, ko kuma bayyana adadin almajiran da aka samu maau ɗauke da cutar, “nasarar da muka mayar da hankali mu samu shine basu kulawa tare da samun lafiyarsu” Ganduje.

Ya ƙara da cewa “kamar yadda muke mayar da almajirai jihohinsu haka muma ake dawo mana da namu jihar Kano.

Kuma wannan matsaya ce da muka cimma mu ya mu ƴan arewa, don haka ba abin surutu bane” inji Ganduje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: