Gwamnatin jihar Kano ta sake sanar da saka dokar zama a gida tsawon mako ɗaya.
Sanarwar da kwamiahinan yaɗa labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba ya fita, ya ce ana yin hakan ne don daƙile yaɗuwar cutar covid 19.
Ya ƙara da cewa ya kamata jama ar jihar Kano su yi haƙuri domin abu ne na wani lokaci.
Sannan ya ce an yi hakan ne bisa shawarar masana don ganin an kare rayuka da lafiyar Al ummar Kano