Shugabannin Kiristoci mabiya darikar Katolika a Najeriya sun gabatar wa gwamnati asibitocin su 425 dake fadin kasar domin amfani dasu wajen killace masu fama da annobar COVID-19.

Sakataren Gwamnatin kuma shugaban kwamitin yaki da cutar Boss Mustapha shine ya sanar da haka bayan gwamnati ta koka kan karancin wuraren da za’ayi amfani da su wajen killace masu dauke da cutar.
Mustapha wanda ya yabawa shugabannin Katolika wajen daukar wannan mataki, yace gwamnatin za tayi amfani su wajen kula da masu fama da cutar.

Majiyar mu ta Rfi hausa ta rawaito cewa Sakataren gwamnatin ya bukaci Gwamnonin Jihohi da su tuntibi shugaban darikar Katolika dake Jiharsu domin karbar cibiyoyin kula da lafiyar.

Rfi