Gwamnan jihar Kano yaa ƙaddamar da cibiyar da aka sakawa suna Daula Female Isolation Center da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a birnin jihar.
Sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar ya ce, gwamnan ya yi hakan ne don samar da nutsuwa ga marasa lafiya tare da bawa kowanne jinsi haƙƙinsa yadda za su samu cikakkiyar kulawa daga ƴan uwansu mata.
An samar da ma aikata waɗanda tuni aka rabasu zuwa gurbin da za su yi aiki a wajen a cewar Gwamna Ganduje.
Sannan ya buƙaci ma aikatan da su kasance masu bawa marasa lafiyan cikakkiyar kulawa a kan lokaci.
Cibiyar killacewar ta Daula Female Isolation Center na ɗauke da gadon kwanciya guda 100.