Gwamnatin jihar Kano ta sanar da killace daliban makarantun allo da aka fi sani da Almajirai 2000 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Kwamishanan lafiyan na jihar Kano Dr Aminu Tsanyawa, ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis a bikin kaddamar da horon ma’aikatan da za’a daurawa nauyin kula da yara a cibiyoyin killacewan.
Ya ce wadanda ake horaswa sun hada da Likitoci, ma’aikatan jinya, da masu gwajin da zasu gwada dukkan yaran.

A cewarsa, an ajiye wadannan Almajirai ne a sansanin killacewa uku a kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da Karaye.

Majiyar mu ta Muryar yanci ta rawaito cewa cewa gwamnati tace Almajiran zasu ci gaba da zama har tsawon Kwanaki 14 domin tabbatar da zargin da ake ko suna dauke da cutar Coronavirus in kuma basuda ita zaa mika kowane gaban iyayensa.