Gwamnan Jihar katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce zaa dage dokar hana zirga zirga da gwamnati ta sanyawa wasu kananan hukumomin a jihar wayanda aka samu bullar cutar Corona a ciki.
Gwamnan yace cikin sati mai zuwa,za’a Sassauta dokar Hana zirga zirga domin al’umma su samu damar yin hidimomin saye-sayen kayan Sallah da yin Sallah idi da Kuma hawan Sallah a jihar Katsina kamar yaddA aka saba bisa al’ada.
Gwamna Masari ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake hira ta musamman da manema labarai a garin Katsina.
Masari ya kara da cewa za su sassauta wannan dokar kuma, Dagewar ba ta kwana daya ba ce ta kwanaki da dama ce.
Da ya juya kan matsalar tsaron da ta addabi wasu kananan hukumomi da suke fama da yan bindiga ya ce a yau asabar za’a samu karin sojoji kasa sakamakon wata tattaunawa da yayi da su a jiya.
Harkar tsaro kacokan tana hannun Gwamnatin Tarayya , saboda sojojin da yan sanda duk hannunsu yake.
Source Liberty/Muryar yanci