Gwamnatin jihar Kano ta ce maau riƙe da muƙaman siyasa za a basu rabin albashinsu saboda annobar Corona.

Sanarwar da Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya futar, ya ce annobar Corona ta sa faraahin man fetur ya faɗi a kaauwar duniya.
Wannan ne dalilin da ya sa maau muƙaman siyasa kamar gwamna, mataimakinsa, kwamishinoni ciyamomi kansiloli da maau bada shawara da mataimaka na musamman a siyasa, za su samu kashi 50 na albaahinsu.

