Kotun tafi da gidanka ta jihar kano ta ci Tarar wani mutum dan Asalin kasar Labanon mai suna Hussain Khalil tarar 200,000.
Kotun karkashin Jagorancin mai sharia Sadiku Sammani, ta kama Hussain da laifin karya dokar Hana zirga zirga a jihar tare da cin zarafin jami’an yan sanda.
Mai magana da yawun kotunan jihar kano Baba jibo ya shaidawa Jaridar Kano Focus cewa mai laifin dai ya tsallake shingen Yan sanda dake titin Ibrahim Taiwo Road tare da zagin jami’an yan sanda.
Nan take suka bishi tare da taimakon jami’an yansandan sashen kula da ababen hawa MTD inda suka kamashi a titin gidan Murtala.
Kotun dai ta kama shi da laifuka har guda hudu wanda kowannensu a ka cishi tarar Dubu hamsin hamsin.
Bayan Wanda ake zargi ya amsa laifinshi.