Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da matakin baiwa al’ummar jihar damar yin sallar Idi.

Gwamnan ya sanar da daukar matakin ne bayan cimma matsaya da Malamai da sauran masu ruwa da tsaki yayin ganawar da suka yi a yau litinin, bisa sharadin daukar matakan kare yaduwar annobar coronavirus yayin gudanar da ibadar ta Sallah Karama. Sai dai ba za a yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba ba.
Gwamnan ya kuma sanar da janye dokar hana yin Sallar Juma’a da aka shafe makwanni ba’a gudanar ba, domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Cikin sharuddan da gwamnati ta gindaya, Sallar Juma’ar za ta rika gudana ne a karkasin kulawar jami’an hukumar Hizbah, wadanda za su tabbatar da cewar mutane sun kiyaye dokokin tsafta da sauran sharuddan da kwararru suka gindaya.

Ganduje ya kuma yi karin bayanin cewar daga yanzu za a sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar ta Kano, inda za a baiwa jama’a damar fita sau uku a mako, a ranakun Litinin, Laraba da kuam Juma’a daga karfe 10 na safiya zuwa 6 na yammaci.