Babban Kotun Tarayya dake birnin yanaguwa Na jihar Bayalsa karkashin Mai Shari’a Jane Iyang,
ta yankewa Yunusa Dahiru(Yellow) hukuncin daurin Shekaru 26 a gidan gyaran hali da tarbiya.

Kotun dai ta kama Yunusa da laifin Sace wata yarinya mai Karancin Shekaru Mai Suna Ese Oruru tare da tilasta aurenta.
Yunusa Dan Asalin jihar kano ne Wanda ya taho da yarinyar daga can jihar Bayalsa zuwa birnin Kano tun A shekarar 2016.

Da yake yanke hukunci a yau Alhamis
Ya yanke hukuncin Mai Shari’a jane iyang kamashi da laifuka daban daban, tare da yanke hukuncin Shekaru 26.
