Daga Bashir Muhammmad

Gwamnan Jihar Imo Hope Odizienma ya soke dokar fanshon gwamnoni da Mataimakansu da shuwagabnni majalisa da Mataimakansu a jihar.

Gwamnan ya soke dokar ne bayan ya aikawa majalisa ta kuma amince dayin hakan,kazalika gwamnan yace yayi amfani da kundin tsarain mulkin Najeriya wajan soke dokar fanshon.
Haka kuma Gwamnan ya kara dacewa kundin tsarin mulki yayi bayanin yadda za’abiya mutum fanshon idan ya fara aikin gwamnati sai ya shekara goma tukunnan zai shiga tsarin cin gajiyar fansho a Najeriya.

Sannan Gwamnan yace tsarin fanshon gwamnoni da mataimakansu da kuma shuwagabanni majalisa da mataimakan su tsarine na zalunci da tsoffin gwamnoni suke tsarawa dan cin moriyar kansu koda bayan sunbar Mulki.
Daga kar karshe ya yabawa yan majalisar da suka amince aka kawar da tsarin handama a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: