An yi hakan ne don rage yaɗuwar cutar Covid 19.

A ƙoƙarin samar da tazara da rage cunkoso a gidajen yari, gwamnan Kano Aabdullahi Umar Ganduje ya yiwa fursunoni 294 afuwa a ranar idi.
Hakan na zuwa ne bayan da shugabaan ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci gwamnoni da su yi afuwa ga wasu daga cikin furaunoni don rage cunkosos a gidajen yari.

Gwamnan Ganduje ya ziyarci gidan gyaran hali da Goron dutse tare da rakiyar muƙarrabansa, bayan sun halarci sallar idi a yau.

Babban sakataren yaɗa labaran gwaamnan Kano Mallam Abba Anwar ya bayyana cewar, gwamna Ganduje ya gabatar da sallar idi tare da mataimakinsa dakta Nasiru Yusuf Gawuna da sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manyan muƙarraban gwamnati .
Kwantirola janar na gidan gyaran hali Magaji Abdullahi ya yabawa tsarin gwamnan Kano ganin yadda yake hoɓɓasa don rage ayyukan laifi a jihar.