Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Kira ga manoman da su kara yawan abincin da suke nomawa, duba da halin da ake ciki, Najeriyar ba ta da kudaden sayen abinci daga kasashen ketare don shigar da shi kasar.

Shugaba Buhari ya you wannan Kira ne ga manoman a ranar Lahadin da ta gabata, jim kadan bayan kammala sallar Idi tare da iyalinsa a Abuja, inda ya taya su fatan samun damina mai albarka.

Shugaban kasa yayi wannan jawabi ne kwanaki kadan bayan gargadin da ministar kudin kasar Zainab Ahmed Shamsuna ta yi a makon jiya,
inda tace babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya durkushe nan bada jimawa ba, muddin annobar coronavirus ta cigaba da yaduwa nan da tsawon lokaci.

Najeriya dai na daga cikin kasashen duniyar da tasirin annobar coronavirus ya fi illata tattalin arzikinsu, duba da cewar kusan kaso 90 na kudaden shigar da kasar ke samu daga danyen mai ne, wanda cutar tayi sanadin faduwar farashin gangarsa a kasuwannin duniya daga kusan dala 60 zuwa kasa da dala 20, Wanda yanzu ya koma dala 30 a kasuwar Duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: