Hukumar lura da kafafen yada labarai ta Najeriya, ta ci tarar gidajen Radio uku a bayan kamasu da laifin karya dokar hukumar.
Tare da yada labaran karya kan Cutar Covid 19.

Babban daraktan Hukumar na Riko Farfesa Amstrong Idachaba shine ya bayyana hakan, a lokacin da yake Ganawa da manema labarai a yau laraba a birnin tarayya Abuja.
Idachaba yace Gidajen Radiyon da aka ci tarar su, sun hada da Adaba Fm,da Breeze Fm, dukkaninsu suna garin Akure, sai Albarka Fm dake Garin Ilorin.

