Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Taya Al’ummar jihar Kano Murnar gudanar Da sallar Juma’a da Idi tun bayan sanya dokar takaita zirga zirga da cunkoso Dan Yaki da Annobar Corona Virus.

Gwamman ya taya Al’ummar jihar Murnar ne a lokacin da yake jawabi gaban Kwamitin dake yaki da Cutar Corona Virus a jihar Karkashin Jagorancin maitaimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, da sauran mambobin kwamitin da mataimaki na ministan Lafiya kan taking da Annobar Covid 19. farfesa Abdussalam Nasidi.
A cewar ganduje ” Muna Taya Al’ummar jihar kano Murnar gudanar da sallar Juma’a da sallar idi karo na farko duk da barazanar Annobar Corona Virus da ake fuskanta,
Muna kuma yabawa limaman masallatan juma’a da yadda suka bada hadin Kai wajen bin Dokokin da aka gindaya a yayin gudanar sallar juma’a da na idi”

Haka kuma gwamnan yace zasu cigada da sa’ido don ganin ana cigaba da bin Dokokin Da aka gindaya a lokacin gudanar da sallolin juma’a da ma wuraren ibada.
Haka kuma yayi alkawarin aiki kafada da kafada da malaman Addinai don ganin an yaki cutar Cutar Covid 19.

Shima a nasa Jawabin mai lura da Kwamitin yaki da Dr Tijjani Hussaini Jami’in A tawagar dake yaki da Cutar Covid 19 a jihar kano ya bayyana alkaluman masu dauke da Cutar a jihar.
inda yace jihar kano yace mutanen da ka gwada sun Kai 4,115 yayin da aka tabbatar da mutane 923 sun kamu da cutar.
An kuma sallami mutane 134 yayin da mutane 38 suka rasu.
PR/AHB