Gwamnatin jihar Kano ta jaddada dokar zama a gida bayan ɗage takunkumin da gwamnatin tarayya ta yi bayan cikar wa adin makwanni biyun da aka saka daga baya.

Cikin sanarwar da ta fito daga kwamishinan yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Muhammad Garba, ya ce iya ranakun da aka ware na Laraba, Juma a, da Lahadi aka sahalewa jama a fita don yin kalaci.

Sanarwar ta ƙara da cewa an saussauta dokar ne a ranar daga ƙarfe biyun da aka saka a baya zuwa ƙarfe shida.

Sannan an bada damar zuwa wuraren ibada a ranakun kamar yadda sanarwar ta cigaba da faɗa.
Haka kuma makarantu za su cigaba da zama a rufe yayin da a yanzu haka gwamnatin Kano ta gayyaci shugabannin kasuwanni a jihar don tattauna batu a kai.
#Mujallarmatashiya