Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cafke mutane 11 da suka yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade a Kasuwar Limawa dake garin Dutsen Jihar Jigawa.

cikin wayanda aka kama har da wani mutum dan shekaru 57,

Haka zalika hukumar ta ce, ta baza komarta wajen neman wasu wadanda suka yi wa wata ‘yar makaranta mai suna Vera Uwaila a jihar Edo fyaden da yayi sanadiyar mutuwarta.

Rfi hausa ta rawaito cewa Kungiyoyin Kare Hakkin Mata sun sha neman a dinga yanke hukuncin kisa kan duk Wanda da aka kama da laifin yi wa karamar yarinya fyade a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: