A yayin da ta kaiwa gwamnan jiharKano ziyara bayan kammala hidimar ƙasa a jihar Kano, Shugaban hukumar shiyyar Kano A isha Tata Muhammad ta ce babu mai ɗauke da cutar ko da mutum ɗaya.

Ta bayyana hakan ne tare da nuna jin daɗinyadda gwamnattin Kano ta kula da su a duk lokacin da sukabuƙaci taimakon hakan.
ta ƙara da cewa yayin da cutar ta ɓulla a kano iyayen ɗaliban na ta kiran waya don jin lafiyar ƴaƴansu, amma ba a samu ko mutum ɗaya mai ɗauke da cutar a cikin ɗaliban ba.

Gwamna Ganduje ya sha alwashin samar da cigaba a hukumar tare da kawo tabbatar da hakan a aikace.
