Gwamnan Jihar Bornon Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dakatar da daukacin jami’an kiwon lafiyar da ke aiki a babban asibitin garin Ngala sakamakon yadda suka kaurace wa bakin aikinsu tare da barin majinyata cikin wani hali.

Lamarin ya faru ne bayan Gwamnan ya kai ziyarar ba zata a asibitin a ranar Litinin da misalin karfe 11 na safe, inda ya tarar cewa, jami’an kiwon lafiyar sun mika ragamar kula da asibitin a hannu Kungiyar Agaji ta fhi360 da ke kula da daruruwan marasa lafiya ‘yan gudun hijira.

Jami’an lafiyar sun kaurace wa aikinsu duk da cewa suna karbar albashi daga hannun gwamnatin jihar Borno a kowanne karshen wata.

Gwamnan ya ce, ,zai sake kai ziyartar asibitin,inda yake fatan ganin sauyin al’amura kafin dawowarsa.

Rfi hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: