Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da gidaje fiye da 20 da aka samar a ruga da ke Ɗansoshiya.

Gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta haramtawa ƴan wasu jihohin ƙasashen Africa ƙetarowa Najeriya don daƙile rikicin fulani a ƙasar.
Tun a baya aka saka harsashin fara ƙirƙirar ruga don samawa fulani matsuguni a wani salo na daƙile rikicin.

Jihohi da dama ne suka buƙaci cin gajiyar ruga wanda gwamnatin jihar Kano ta samar har ma ta ƙaddamar a yau.

Kafin annobar corona dai rikicin fulani ne ke kan gaba cikin matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.