Rahotanni daga Bankin raya kasashen Afrika AFDB ya ce ya baiwa Najeriyar rancen dala miliyan 288 a ‘yan tsakanin nan don taimakawa kasar farfadowa daga illar da annobar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikinta.

Gabanin ikirarin bankin na AFDB ko a watan jiya ministar tattalin arzikin Najeriyar ta bayyana yiwuwar tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya da kashi 9 sanadiyyar annobar ta COVID-19.
Wanda dole ta tilasta kulle muhimman sassan kasuwanci da tattalin arziki baya ga farashin danyen man fetur da ya fadi a kasuwar duniya.

Rfi hausa ta rawaito cewa Ko cikin watan Afrilu Najeriyar mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika sai da ta karbi makamancin lamunin farfado da tattalin arzikin daga asusun bada lamuni na duniya IMF da yawansa ya kai dala biliyan 3 miliyan dari 4.

#Copy