Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Muhammad Alfa mai kimanin shekaru 31 da ya kware wajen yin kwartanci da aikata fyaɗe.

Kakakin hukumar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da cewar sun kama matashin a garin ɗan gora da ke Kano.
Mataahin dai ya kware wajen aikata fyaɗe,kwartanci wanda ya yiwa mata sama da 40 a shekkara guda.

Cikin mutanem da yake yiwa fyaɗe akwai tsofaffi da ƙananan yara.

Tuni kwamishinan ƴan samdan ya bada umarnin aike da matashin zuwa sashen binciken manyan laifuka don zurfafa bincike.
Duk da cewar matashin ya amsa laifinsa,za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.