Gwamnan jihar Kano yaa ƙaddamar da wuraren gwajin cutar numfashi ta Covid 19 a kano.

Gwamnan jihar Kano Ganduje ya buɗe wuraren wanda waɗansu ƙungiyoyi biyu suka kafa a wani salo na shawo kan annobar a jihar

Wuraren dai za su ɗauki sampilin gwajin mutane 390 a kullum, sannan za su fara aiki ba da jimawa ba.

Mataimakin daranktan operation of E-Health Africa Mista Atif Fawaz ya ce ganin ƙoƙarin gwamna kan shawo kan lamarin ne ya ja hankalinsu har suka ɗauki nauyin samar da cibiyar gwajin.

Shima mista Barnand Eburuka  da ya wakilci ƙungiyar International  Foundation against infectious diseases in Africa ya ce ƙungiyar ba ta da wani buri illa samar da hanyar shawo kan wata annoba da ke yaɗuwa a cikin al umma.

Gwamnan ya buƙaci al umma da su cigaba da bada gudunmawa a dukkan lamarin al umma ba iya cutar covid 19 ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: