Sashin Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar tara Dala miliyan 182 domin tallafawa mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya da rikicin Yan Tada kayar baya ya daidaita.

a sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun Kelechi Onyemaobi tace tana bukatar kudaden cikin gaggawa domin kai dauki ga miliyoyin mutanen da rikicin tare da annobar coronavirus ta shafa.

Sanarwar tace hukumar ta damu matuka da halin da irin wadannan mutane ke ciki a Jihohin Adamawa da barno da Yobe wadanda ke fuskantar tsananin yunwa, yayin da wasu ke cikin yanayin kakani kayi.

Hukumar ta bayyana yankin a matsayin daya daga cikin yankunan duniya dake fuskantar matsalar abinci da sauran kayan bukatu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: