Gwamna jihar Kano ya tabbatar da ƙara ranar litinin a matsayin ranar da za a fita don sararawa a kano.

Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar,gwamnan ya ce ya ƙara sassauta dokar ne don bawa jama ar kano damar rage zaman da ake yi na hana yaɗuwar cutar a cikin al umma.
Ganduje ya ce ya zama wajibi kasuwanni da wuraren da aka amincewa buɗe wurarenau su bi sokokin kariya da aka saka na hana yaduwar cutar.

A kwananan ma gwamna Ganduje ya amincewa maau gidajen kallon kwallon ƙafa su buɗe gidajen kallonsu, yayin da makaranatu suka ci gaba da zama a kulle.