Shugaban ƙungiyar kafafen yaɗa labarai a jihar kano kuma shugaban gidajen rediyon Cool, Wazobia, Arewa Prince Aboki ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka yi a Africa House.
Ya ce ya zama wajibi a jinjinawa gwamnan ganin yadda yake bawa ƴan jarida haƙƙinsu ta hanyar basu damar gudanar da aiki yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa saɓanin wasu jihohi da za a iske ana cin zarafin ƴan jarida tare da hanasu gudanar da aikinsu.
Prince Aboki ya tabbatar da cewar a shekaru biyar na gwamnatin Ganduje, babu wani ɗan jarida da aka ci zarafinsa ko hanashi gudanar da aikinsa.