Shugaban kasa Muhamadu Buhari yayi Kira ga Al’ummar Jihar Katsina da suyi hakuri kan irin Abubuwan dake faruwa a jihar na ta’addanci.

A cewarsa gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen yaki da yan bindigar da suka addabe su, ya kuma jajantawa wadanda suka rasa yan uwan su, da Dukiyoyinsu.
Wannan Jawabin ya fito ne beta cikin Wata sanarwa da , mai Magana da yawun Shugaban Buhari Malam Garba Shehu ya fitar tare da rabawa manema labarai.

ya kuma bukaci al’ummar Jihar da su cigaba da goyawa sojoji baya domin samun nasara kamar yadda suka samu a shekarun baya.

Buhari yace tuni jami’an tsaro suka gano maboyar Yan bindigar a dajin dake Arewa Maso Yammacin kasar kuma zasu kawar da su daga ciki.
, ganin yadda aka inganta bincike da leken asisri, yayin da jiragen yaki na kai hare hare har cikin dare.
A yau mazauna Jihar Katsina sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin ran su da yadda Yan bindigar ke cigaba da hallaka su ba tare da kaukautawa ba.