Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Rundunar ƴan sanda ta cafke wasu ƴan Karota uku a Kano

Rundunar ƴan sanan jihr Kano ta cafke wasu ƴan karota uku a Kano baan zargin lakaɗawa wani mutum duka har takai ga sun karyashi.

Mai magana da yawun ƴan sanda a kano DSP Abdullahi Harun Kiyawa ne ya bayana hakan ga manema labarai.

Ya ce an samu rashin jituwa tsakain ƴan karota da wani Aminu Abdullahi wanda hakn ya sa jama a suka farwa jami an Karota.

Ya ƙara da cewa tuni aka kai mara lafiyan asibitin Murtala kuma an kama mutane uku ƴan karotan wanda ake bincike a kansu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A. Sani ya gana da shugaban hukumar tare da bashi shawarar horas da jami ansu don samun kwarewar aiki da al umma.

Kakakin ya jaddada cewar har kullum ƴan sanda a shirye suke wajen kare rayuka da lafiya da ma dukiyoyin al umma.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: