Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

GIDAUNIYAR ISLAND SURVIVE FOUNDATION TA KAI AGAJI A KANANAN HUKUMONIN DUTSINMA, SAFANA DA DANMUSA

DAGA RABIU SANUSI KATSINA

A yunkurin rage radadi da agaji ga marayu da ma su karamin karfi kungiyar fafutukar ganin an taimaki marassa galihu da aka sa ni da Island survive foundation da ke da ofishin ta a jihar Kaduna da katsina,
ta yi taron gangamin bude ofishin ta na shiyyar katsina ta tsakiya agarin Dutsinma kwanan baya.

Haka zalika yayin bude ofishin kungiyar ta fara bada tallafi ga marayu da gajiyayyu a kungiyance daga kananan hukumomi ukku da su ka hada kungiyoyi biyu daga cikin karamar hukumar Dutsinma sai daya daga Safana cikon kungiya ta ukku kuma daga karamar hukumar Danmusa.

Tallafin da ya hada da kayan abinci da su ka hada da Masara, Gero, Wake da shinkafa sai atamfofi.

A na shi jawabin shugaban gidauniyar Dr, Muhammad Bara’u Tanimu ya bayyana cewa aikin wannan kungiya ne duba mutanen da su ka cancanta kafin a mika tallafin.

Dr Bara’u ya kara da cewa kafin mika tallafin sai da aka tabbatar kungiyoyin sun tantance marayu na gaskiya kuma aka duba yankin da matsalar tsaro ya shafa da wadanda abin ya shafa sannan aka damka musu Tallafin.

Haka kuma ya bayyana cewa sun fara bada wannan tallafin ne a yanzu kuma za su ciga da badawa a sauran gurare ba.

Su ma wadanda su ka amfana da tallafin gidauniyar ta island survive foundation sun nuna matukar godiyar su tare da yiwa wannan gidauniya addu’o’in samun nasara da zaman lafiya da cigaba musamman ga shugabannin tafiyar da iya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: