Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmadu sani ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi a wajen taron kafa kwamitin shawara kan haɗakar ƴan samda da al umma.

 

Ya cigaaba da cewa “na mai farin ciki tare da yi muku maraba, yayin da muke kafa wannan kwamitin shawara na musamman a wannan gunduma (Area Command) kan shirin hadaka tsakanin al’umma da hukumar ‘yan sanda da akai wa take da (ACPAC). Wannan wata gagarumar nasara ce, tsarin hadakar zai tabbata a jihar kano domin samar da cigaba ta fannin tsaro ga aikin hukumar ‘yan sanda a jihar kano.

  1. Mun samu nasarori masu dimbin yawa a tsarin gudanar da aikin tsaro a jihar kano, kuma wadannan nasarori sun samu ne sakamakon wannan sabon yunkuri na hadaka tsakanin hukumar ‘yan sanda da al’umma, karkashin jakorancin mai girma Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Mohammed Abubakar Adamu, NPM, mni tare da kokarin hukumar na ganin cewa an yaki kowanne irin nau’in aikin barna a cikin kasa baki daya wanda jihar kano tana daya daka ciki.

  2. Shirin Hadaka tsakanin hukumar ‘yan sanda da al’umma shiri ne na hadin gwiwa tsakanin hukumar yan sanda da kuma al’ummar dake iya ganowa tare da magantar matsalolin da suke kewaye da ita, hikima ce da take habbaka tsare tsaren kungiyoyin da suke hada karfi da karfe domin shawo kan matsalolin da suke cikin al’umma na tsaro takan amfani da hanyoyin zamani masu inganci, da samar da yanayi na lumana da aminci daga barna, rashin zaman lafiya da kuma tsoron da ke faruwa sakamakon barkewar barna ko aikata laifuka.

  3. Tuni Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Kaddamar da Kwamitin Shawara na jiha, karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero. Yanzu za’a kaddamar da kwamitocin Gunduma (Area Command), Karamar Hukuma da kuma na Chaji Ofis (Division), wadanda suna da aiki kamar haka:-

i. Kwamitin shawara kan shirin hadakar hukumar yan sanda da al’umma na Area Command (ACPAC) kwamitine da zai dinga tattaunawa akan shirin cikin yankin da ke aiki a karkashin kulawar area command, kwamitin zai hada da DPOs, Ma’aikata daga wasu sashen tsaro na musamman, da kuma al’ummar wannan yankin da zasu zama masu samar da dukkan bayanan da ake bukata akan sha’anin tsaro don samar da zaman lafiya, lumana da kuma sulhu.

ii. Kwamitin shawara kan shirin hadaka tsakanin hukumar yan sanda da al’umma na karamar hukuma (LGCPAC) kuma, shine zai kula da shirin a kananan hukumomi, kwamitin zai yi aiki tare da Shugaban Karamar Hukuma domin samar da kyakyawan tsarin wayar da kai ta fuskar tsaro, da kuma dukkan abinda zai taimaka wajen tabbatar da tsarin daga tushen sa don samar da ingataccen yanayi na zaman lafiya. Kwamitin zai dinga bada rahotonsa kai tsaye ga Kwamitin Shirin hadakar na jiha (SCPC).

iii. Kwamitin hadaka tsakanin hukumar yan sanda da al’umma na kowanne division zai kasance da masu unguwanni (Mai gari) ko jagororin al’ummar wannan yankin, wanda zasu kasance tare da masu tantance wadanda za a dauka daga al’ummar don kasancewa a matsayin constable a cikin unguwannin da suke. Wadannan matasa da aka dauka a matsayin constable a unguwa/ kauye zasu zamanto jakadun samar da zaman lafiya, samar da aminci, wayar da kan al’ummar akan sha’anin tsaro, tattara muhimman bayanai da bincike na musamman, yaki da matsalolin da suka addabi yankunan su, da kuma yin sulhu ga sabani da kuma kananan laifuka. Kwamitin zai sanya idanu akan yadda ake gudanar da aiki a yankin, tabbatar da ya gudana a irin yadda hukumar yan sanda ta tsara tun daga tushe har zuwa matakin karshe domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
5. A karshe, wadannan kwamitoci an kaddamar dasu. Wadanda aka basu wannan dama, dafatan zasu rike amana tare da taimakawa al’umma domin inganta harkar tsaro a jihar Kano. Allah ya baku ikon taimakawa. Muna mika godiyar mu ga mai girma gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, OFR na irin gudun mawar da yake bawa rundunar ‘yan sandan jihar kano, muna godiya ga mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa kokarinsa na ganin an samu ingantaccen tsaro a jihar kanon da kasa bakidaya. Ina kuma godiya ga dukkan al’ummar Jihar Kano na bada hadin kai, kyakywar fahimtar su da kuma bin ka’idojin da hukumar yan sanda ta Jihar Kano ta sanya musamman a wannan yanayi na kwararowar annobar cutar Covid-19. Duk wadanda suka halarci wannan taro, muna fata Allah (SWT) ya maida kowa gidansa lafiya Amin.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: