alamu na nuni da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya ji a jikin sa cewar ba zai samu nasarar zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Nuwamba ba, sakamakon yadda sau biyu a wannan mako yana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zabe mai zuwa.

A wata hira da yayi ta tashar Fox News, shugaba Donald Trump ya nuna alamun bada kai bori ya hau, inda yake cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden zai kada shi a zaben watan Nuwamba mai zuwa.

A hirar Trump yace Biden zai samu nasarar ce saboda wasu mutane basa son sa a Amurka, kuma wannan shi zai baiwa tsohon mataimakin shugaban nasara.

Rfi hausa ta rawaito cewa Trump yace Biden zai zama shugaban kasa ne kawai saboda wasu Amurkawa basa son sa, kuma shi babu abinda yake sai gudanar da ayyukan sa kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: