An yabawa wa Kwamishinan yan sandan jihar Kano Habu Ahmadu Sani wajen Samar da tsaro a jihar Kano dama masarautar Rano.

Mai martaba Sarkin Rano Alh Kabiru Mohammad Inuwa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke Mika lambar yabo ga Kwamishinan yan sandan.
A cewar Sarkin Kwamishinan yan sandan jihar Kano ya bada gudunmmawa wajen Samar da tsaro da kyakkyawan yanayi a masarautar Rano. Ta hanyar kakkabe bata gari da suka addabi yankin.

Ya kuma ce masarautar Rano a shirye take wajen aiki da jami’an yansanda goyon baya akan aikin su na tabbatar da tsaro Dari bisa Dari.

Ya kuma yi Kira ga wayanda aka rantsar da su rika taimakawa jami’an yansanda, da suyi aiki tsakaninsu da Allah da kuma bada hadin Kai wajen Samar da tsaro da kawar da bata gari a fadin jihar Kano.
Shima anasa Jawabin Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Habu Ahmadu sani wanda ya rantsar da masu taimakawa yan sanda a fannin tsaro na na cikin Al’umma.
A cewarsa Rundunar yan sanda ta samu nasarori da dama da taimakon yan San cikin Al’umma. Wato Community Policing.
Rundunar tayi nasarar cafke wasu bata gari a lokacin da Annobar Corona ta barke inda Rundunar tayi nasarar cafke wayanda ake zargin da fashi da makami su 18, da bakwai masu garkuwa da mutane,Sai wayanda ake zargin da Zamba cikin aminci su 10, yayin da aka Rundunar yan sandan tayi nasar cafke Mutane 14 da zargin safarar miyagun kwayoyi. Da yan daba su 317 an kama su a wurare daban daban da muggan makamai da harsashi 1289, an kuma kama su day motoci 4 babura Mai kafa uku da sauran miyagun kwayoyi.
. Kwamishinan ya bayyana cewa dukkan wannan nasarori an samu ne da gudunmmawa Al’ummar ta hanyar basu hadinkai da kuma bayyana maboyan bata garin.