Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Covid 19 – Gwamnatin tarayya za ta ƙara saka dokar zaman gida a Kano, Katsina, Legas da Abuja

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar akwai yuwuwar saka dokar kulle a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihohin ƙasar masu rinjayen waɗanda ke ɗauke da cutar Covid 19.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar Covid 19 Boss Mustapha ne ya bayyana hakan yayin da ya gabatarwa da shugaban ƙasa rahotansa a ranar litinin.

Cikin ƙananan hukumomin da cibiyar daƙile yaɗuwar cutuka a Najeriya NCDC ta bayyana akwai ƙaramar hukumar Nassarawa da Tarauni a Kano, da ƙananan hukumomin Mushin, Eti-Osa, Alimosho, Kosofe,Ikeja, IshodiIsolo, Apapa,Amuwo, Odofin, Lagos Island, da Surulele a jihar legar.

Sauran sune Abuja Munincipal a babban birnin tarayya Abuja.

A jihar Katsina kuwa akwai ƙaramar hukumar Katsina, sai jihar borno  a Maiduguri sai ƙaramar hukumar dutse a jihar jigawa.

A baushi akwai ƙaramar hukumar Bauchi sai oredo a jihar Oredo, sannan Ado/Ota a jihar Ogun.

Gwamnatin na duba yuwwar saka dokar kulle a ƙananan hukumomi 18 zuwa ashirin cikin ƙanan hukumomin 774 da ke jihohin Najeriya

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: