Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran ƙasa

Gwamnatin Tarayya ta janye Dokar Hana Tafiye Tafiye

Daga Maryam Muhammmad

Gwamnatin tarayya ta janye dokar hana tafiye-tafiye a fadin kasar nan sannan ta bada umarnin a bude makarantu don ‘yan ajin karshe su koma makaranta.

Dokar zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli 2020.

Bisa ga dokar gwamnati ta amince wa mutane su yi tafiya da a lokutan da babu dokar hana walwala.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 Boss Mustapha ya Sanar da haka a taron da yayi da manema labarai a Abuja.

Ya ce gwamnati ta bude makarantun ne domin daliban da ke ajin karshe su fara bita da kuma shirin yin jarabawa.

Bayan haka Mustapha ya kuma ce gwamnati ta kara makonni hudu a karo na biyu na dokar dakile yaduwar cutar Korona a fadin kasar nan.

Dokar zai fara aiki ne ranar 30 ga watan Yuni zuwa 27 ga watan Yuli 2020.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar zaman gida dole a karon farko da ya yi tsawon makonni biyar a Abuja da jihohin Legas da Ogun.

Dama kuma gwamnati ta sanar da cewa daga wannan mako za ta fi maida hankali a kananan hukumomin da cutar ta fi tsanani ne.

Ya ce a wadannan kananan hukumomi za a saka dokoki da zai sa a tunkari wannan annoba ta hanyar tsananta gwaji da samar musu da kula.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: