An yi Kira da Matasan jihar Kano da su guji harkar ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauran Al’ amuran bata gari.

Kiran ya fito ne ta bakin Shugaban wata kungiyar matasan kano dake wayar da kan matasa kan aikata miyagun laifuka Comrade Abdurahman na malam Ya’u (Kano youth awareness on crime prevention and control)a turance.
Comrade Abdurahman ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar ta kawo ziyara Mujallar matashiya.

A cewar comrade Kungiyar ta samu nasarori daban daban ta hanyar wayar wa matasa kai akan shiga munananan halaye.

Ya kuma ce Kungiyar ta samo wa matasa ayyukan yi da sana’oi ta bangarori daban daban.
Shima anasa Jawabin Shugaban Mujallar matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ya yabawa Kungiyar da irin ziyara da ya kawo Ofishinta.
Inda yace dama Mujallar matashiya ta matasa ce dukkanin Al’amura ta tafi mayar da hankali kan cigabar matasa.
Daga karshe Abubakar Murtala Ibrahim yayi alkawarin bawa Kungiyar Goyon baya da kuma gudunmmawa ta bangarori daban daban.