Akalla yan 790 Najeriya sun kamu da cutar coronavirus a rana guda, abinda ya janyo adadin Yan kasar da suka kamu da cutar zuwa 26,484, haka kuma 603 sun mutu.

Hukumar dake yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC tace daga cikin sabbin mutanen 790, 166 sun fito ne daga Jihar Delta, sai 120 a Lagos, 66 a Enugu, 65 a Abuja, 60 a Edo, 43 a Ogun da kuma 41 a Kano.

Sauran sun hada da 39 a Kaduna, 33 a Ondo, 32 a Rivers, 29 a Bayelsa, 21 a Katsina, 20 a Imo, 18 a Kwara, 11 a Oyo, 10 a Abia, 6 a Benue, 4 a Gombe, 2-2 a Yobe da Bauchi da Kebbi.
Zuwa yanzu dai wasu jihohin sun Zanye dokar Hana zirga zirga baki daya ciki harda jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: