Gwamnatin jihar Kano ta sake zaftarewa ma’aikata wani kaso na cikin albashin su.
Idan ba manta ba a watan da ya gabata ma hakan ta faru har aka samu yarjejeniyar da kungiyar kwadago tayi da gwamnatin.
Wasu ma’aikatan sun tabbatar da sake cire musu kaso cikin albashin su na watan Yuni.
An dai zaftare albashin na Ma’aikatan daban daban inda wasu aka zaftare musu 3000 yayin da wasu Dubu 7000 ya dai danganta da Matakin albashin mutum
Kwanaki kadan da suke wuce dai kungiyar kwadago karkashin shugaban ta Kwamared Kabiru Ado Minjibir suka cimma matsaya da gwamnatin Kano kan janye yajin aikin jan kunne na kwana 7 da suka shirya biyo bayan zaftare albashin watan da ya gabata na.
Sai gashi a wannan wata ma gwamnatin ta sake zaftare albashin ko wane irin Mataki Kungiyar kwadagon zasu dauka ?.