Hukumar dake yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ta ce an samu karin mutane 454 da suka kamu da cutar coronavirus a ranar Juma’a, abinda ya kai jumillar adadin zuwa dubu 27 da 56
Daga cikin jihohi 18 da aka samu karin wadanda suka kamun, Legas ke kan gaba da mutane 87, sai Edo mai 63, Abuja na da 60, 41 a Ondo.
Zuwa yanzu mutane dubu 11 da 69 suka warke daga cutar a Najeriya, yayinda 628 suka mutu.
Rfi hausa sun Rawaito cewa Akalumma na nuni da cewar kusan watanni biyar bayan bullar annobar coronavirus a Najeriya,
Legas ke kan gaba tsakanin jihohin kasar wajen yawan wadanda suka kamu da cutar da adadin mutane dubu 10 da 910, Sai Mai biye mata birnin Abuja ne da mutane dubu 2 da 80, sai kuma jihar Oyo mai mutane dubu 1 da 451.