Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya sanar cewa sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa ya warke daga cutar coronavirus.

Akeredolu ya rubuta hakan ne jiya litinin a shafin sa ta twita,

Inda ya mika godiyar sa ga dukkan mutane da suka rika bin sa da addu’o’in Allah ya bashi lafiya a lokacin da yake kwance.

Sannan kuma gwamna Akeredolu ya kara da cewa har yanzu gwamnati bata na nada sabon kwamishinan kiwon lafiya ba sai mai bashi shawara kan harkokin kiwon lafiya ne ke rike da ofishin kafin gwamnati ta nada wani sabo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: