Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aika wa Majalisar Jihar sunayen kwamishinoni uku da ya zaba domin samun amincewar majalisar.

Kakakin Majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Talata kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gafasa ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar domin nada Idris Garba a matsayin kwamishina kuma mamba na Majalisar Zartarwa na Jihar Kano, SEC.

Gwamnan ya nada sabbin kwamishinoni uku.
Ya ce gwamnan ya kuma nemi yan majalisar su tabbatar da nadin wasu kwamishinoni biyu a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na jihar, KANSIEC.

Tabakinshi, ana sa ran Garba zai bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin a tantance shi.

Ya bukaci wanda zai zo tantancewar kada ya taho da yan rakiya fiye da biyar don bin dokokin kare yaduwar COVID-19.

Malam Gafasa ya mika sunayen kwamishinonin na KANSIEC ga kwamitin majalisar ta Harkokin Zabe don gudanar da bincike a kansu tare da mika rahotonsu a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Litinin ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya gabatar wa majalisar kasafin kudin shekarar 2020 da aka yi wa kwaskwarima domin samun amincewarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: