Gwamnatin Najeriya ta janye matakin ta na sake bude makarantu domin bai wa daliban da ke shirin kammala karatu daukar jarabawa.

Ministan ilimi Adamu Adamu ne ya bayyana hakan inda ya ce sakamakon wannan mataki da gwamnati ta dauka, babu wani dalibin Najeriya da zai rubuta jarabawar kamala karatun sakandare WAEC.

Tun farko dai Hukumar kula da shirya jarabawar ta shirya farawa ne daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba mai zuwa.

Ministan yace babu wani shiri na sake bude makarantun yanzu haka, saboda haka babu ranar gudanar da wannan jarabawa ta kammala karatun Sakandaren bana.

Majiyar mu Ta Rfi hausa ta Rawaito cewa Ministan yace Hukumar WAEC bata da hurumin sanya ranar da za’a bude makarantu a Najeriya domin kuwa ba hurumin ta bane, inda yace gwamnati ta gwammace daliban Najeriya su kara shekara guda a mai makon su kamu da Cutar Cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: