Duba da yawan samun Rahotannin Fyade musamman kananan ‘yan mata a Kano.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta Gudanar da bincike akan wannnan matsala inda ta gano cewa mafi yawan laifukan Fyade ana aikata su ne a kwangaye. Wato ginin da ba a gama gina shi ba,
A don haka gwamnatin Kano ta bada Umarnin cewa duk wani mai tsohon kango a jihar to ya gine shi ko kuma a daure shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka ranar Alhamis.
Haruna ya ce a dalilin haka jami’an tsaro za su rika bin duk wani kagon gini dake jihar suna cafke wadanda ke boyewa ciki suna tafka barna.
” Duk wanda aka kama da laifin aikata wani mummunar abu a irin wani kangon gini, toh laifin zai shafi harda mai mallakin wannan gini.
Haruna ya yi kira masu irin wadannan gine-gine a jihar da su gaggauta gine su tun da wuri.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa a tsakanin watannin Janairu zuwa Mayu 2020 an yi wa mata 42 fyade kuma duk suna gaban kuliya.
Sannan kuma akalla kashi 33.3 bisa 100 na aukuwa ne a ire-iren wadannan kangon gini da ba a kammala su ba.
Kashi 17.7 a gonaki, 15.6 a shaguna, 15.6 a dakuna sannan kashi 8.9 a makarantun kashi 2.2 kuma a kasuwani.
Daga karshe yace rundunar Yan sanda a shirye take ta bankado duk wasu masu aikata laifuka a jihar Kano.