Connect with us

Labaran ƙetare

Yan Amurka Na cigaba da Rasa ayyukan yi Saboda Cutar Corona

Published

on

Yan Amurka da dama ne suka rasa ayyukan su a Amurka saboda Cutar covid 19

Annobar na cigaba da sake raba mutane miliyan guda da Dubu Dari Uku da ayyukan su a kasar Amurka.

Wannan alkaluma na zuwa ne sakamakon cike takardun neman tallafin rasa aiki da suka gabatar a mako guda da ya gabata.

Wannan ya nuna raguwar da aka samu daga miliyan guda da 44,000 da aka samu kusan kowanne mako kamar yadda hukumar kula da kwadagon kasar ta gabatar.

Masana tattalin arziki da kuma ofishin kasafin kudin Majalisa yace zai dauki shekaru kafin kasar ta koma yanayin da take kafin samun wannan annoba.

Amurkawa da dama ke ci gaba da yin Allah wadai ganin ta yada Shugaban kasar Donald Trump ke kawar da idanu tareda daukar matakai dake kawo cikas ga mutanen dake neman ayyukan yi a Amurka.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran ƙetare

Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu

Published

on

Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.

Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.

Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.

Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Awanni Huɗu Kullum A Arewacin Gaza

Published

on

Ƙasar Isra’ila ta amince a tsagaita wuta na awanni huɗu a kullum a arewacin Gaza, don a bai’wa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Fadar gwamnatin Amurka ce ta sanar da hakan a yau Alhamis, duk da cewa shugaban ƙasar Joe Biden ya ce babu cikakkiyar tsagaita wuta.

Biden ya yabawa Fara-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa ɗan dogon hutu a faɗan, bayan tsawon wata daya da aka ɗauka ana fafata rikicin.

Sojojin Hamas da Isra’ila yanzu kowanne yana maɓoyarsa, kusa da inda ake gwabza faɗan a birnin Gaza, a yankin arewacin Zirin Gaza.

Mai magana da yawun sashin tsaron ƙasar  John Kirby ya sanar da manema labarai cewa, Isra’ila za ta fara Ƙaddamar da Dakatar da faɗan na awanni huɗu a kullum a yankin na Arewacin na Gaza.

“Isra’ilawa sun sanar da mu cewa, ba za a samu aikin sojin su a yankin ba na tsawon lokutan da aka ɗauka, kuma hakan zai fara daga yau.”

Continue Reading

Labaran ƙetare

An Sake Cafke Tsohon Shugaban Ƙasar Gini Bayan Ya Tsere Daga Gidan Yari

Published

on

An sake cafke tsohon shugaban gwamnatin soji ta ƙasar Gini Moussa Dadis Camara a jiya Asabar, bayan ya tsere daga babban gidan yari a Conakry babban birnin ƙasar.

Shugaban sojojin ƙasar ta Gini Ibrahima Sory Bangoura ya tabbatar da hakan, ya kuma ce Camara yana cikin ƙoshin lafiya, kuma an mayar da shi gidan yarin na Conakry.

Ya kuma ce an kuma cafke mutane biyu da suka tsere tare da shi, wato Moussa Tiegboro Camara da Blaise Gomou. Kuma an mayar da su gidan yarin su ma.

Sannan sojojin sun bayyana cewa, ana ta ƙoƙari don ganin an kamo ragowar ɗayan da suka tsere tare, wato Claude Pivi.

Kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar wacce ta ke a Conakry, ta bayar da umarnin a yi cajin su da babban laifi dukka su huɗun.

Moussa Camara dai ya Ƙaddamar da juyin mulki a ƙasar, ranar 23 ga watan Disambar shekerar 2008. Wanda kuma ya zama shugaban gwamnatin sojojin ƙasar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: