Ma’aikatar inshoran Manoman Najeriyi tare da hadin gwiwar kamfanin Samar da Abinci na Dantata sun shirya hanyoyin da zasu inganta inshoran Manoman Najeriya.

Wannan jawabi na kunshe ne cikin Jawabin da Manajan Ma’aikatar inshoran Manoma Reshen jihar Kano Alhaji Danladi Mato yayi a lokacin da yake Karin haske shugabannin Kamfanin.

Danladi yace na daya daga jihohin da suke mafi rinjayen Manoma a Najeriya, Wanda suke bada gudunmmawa wajen inganta harkokin noma da habbaka Tattalin Arzikin kasa.

Inda yace da taimakon Masana’antun harkokin noma irin su Dantata sun inganta rayuwar manoma ta hanyar yi musu inshora Dan tallafawa kananan Manoma.

Shima a Nasa Jawabin shugaban rukunin Kamfanonin Dantata Alhaji Tajudden Aminu Dantata ya tabbatar da cewa Kamfanin sa zasu bada hadin kai don ganin Manoma sun samu Amfanin wannan shiri ta hanyar hadin kai a tsakanin Manoma.

Alhaji Tajudden Aminu Dantata yace Kamfanin Dantata zai tabbatar ya bada hadin kai wajen tallafawa Al’ummar kasa tare da Samar da ingantattun Abinci da Samar da aikin yi da kuma Samar da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: