Daga jamilu Lawan Yakasai

Shugaban Kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya gargaɗi ministoci da manyan jami’an hukumomin gwamnatinsa su kyautata alaƙa da majalisar tarayyar Najeriya.
Wata sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar.
Inda yace Buhari na cewa ba zai lamunci duk wani rashin mutunci ga majalisa daga duk wani jami’in ɓangaren zartarwa ba.

Jan kunnen na zuwa ne lokacin da yake ganawa da shugabancin majalisun tarayya a jiya Alhamis, inda suka tattauna game da wasu ayyukan baya-bayan nan na majalisa.

Shidai wannan jan kunnen na zuwa ne sa’o’i bayan shugaban hukumar raya yankin Neja Delta, Daniel Pondei ya fice daga zauren sauraron jin bahasi game da bincike kan harkokin kuɗin hukumar.
Sanarwar fadar shugaban ƙasa ta umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati su tafi da harkokinsu ta yadda ba za su yi zagon ƙasa ga majalisa da shugabancinta gami da wakilanta ba.