Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ana zargin fashewar wani abu da ake tunanin bom ne a jihar.

Rundunar ta ce mutane biyar ƴanƴan wani mutum guda ne suka rasu yayin da shida suka jikkata a dalilin abin gmfashewar.
S P Gambo Isah ya bayyana cewar rundunar ta duƙufa don bincike a kan lamarin, yayin da sashe daban daban na rundunar suka duƙufa don gano sababin lamarin.

Abin fashewar ya fashe ne a wata gona da ke Yammawa a ƙaramar hukumar malumfashi ta jihar Katsina.
