Dakarun sojin Najeriya dake aikin ‘Operation WHIRL STROKE’ sun ceto Mutane 34 da aka yi garkuwa da su sannan sun kwato makamai da dama a jihar Benuwai.
Sakataren yada labarai na rundunar sojin Najeriya, John Enenche shine ya hakan a wata takarda da ya fitar aka raba wa manema labarai a jiya.
Enenche ya ce rundunar ta yi nasarar ragargaza wadannan maharan ne bayan samun bayanan sirri na ayyukan su.
Ya ce a ranar 16 ga watan Yuli dakarun sun farwa maboyar mahara dake kauyen Tomayin inda Suka kashe shugabannin kungiyoyin wanda a ciki akwai wani mai suna Zwa Ikyegh sannan sauran mabiyan kungiyar sun gudu bayan an Raunata su harsashi a jikin su.
Dakarun sojojin sun kwato bindigar kirar AK 47 guda daya, kananan bindigogi guda bakwai, harsashen bindiga, babura biyu da layukan wayoyi dabam-dabam.
Daga karshe Enenche ya ce dakarun sojojin na tsare da maharan da zarar sun kammala bincike a kan su za su danka su hannu Rundunar ‘yan sanda.


