Daga Jamil Lawan Yakasai

Rundunar yan sandan Jahar Kaduna sun cafke maza biyar bisa zargin su da yin lalata da yarinya mekimanin shekaru 10

Matasan da sukafito daga karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna sun ceci yarinya mai shekara 10 da haihuwa da wasu maza biyar su ke kwanciya da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda su ke lalata da karamar yarinyar har da mijin goggonta.
Mahaifin yarinyar nakasasshe ne wanda ba ya iya motsi.

Yanzu haka yarinyar da aka nemi 6ata mata rayuwa ta na karkashin kulawar Hajiya Rabi Salisu ta kungiyar Arida Foundation of Nigeria (AFN).

Haj Rabi Salisu wanda ta fito a wani fefen bidiyo da yanzu haka ke zagaye Duniya wanda yarinyar ta bayyana cewa mahaifiyar yarinyar sun rabu da mahaifinta.

Rabi Salisu takara da cewar yarinyar ta samu kanta a cikin wannan hali ne bayan mahaifiyarta ta kai ta kara wajen mijin ‘yar uwarta saboda ba ta zuwa talla idan aka tura ta.

Shi dai Bawan Allah ya yi amfani da damar da ya samu na kwabar yarinyar, ya kare da kawo wasu ‘yan uwansa har maza biyu wanda su ka rika lalata da yarinyar.

Daga baya wannan Baiwar Allah ta kai kuka wajen mahaifiyarta cewa ta na ganin jini idan ta yi bawali. Daga nan ne tsohuwarta ta ja-kunnen mijin yayartan da ya yi nesa da diyarta.

“Bayan ta koma ta cigaba da talla, sai kuma ta hadu da wani mutumi mai saida gwanjo, wanda ya saya mata takalmin zuwa makaranta, ya rika yin lalata da ita.”

“ Daga nan ne kuma sai wani mutumi mai gidan burodi ya shiga sahu, bayan ya saye shinkafar da ta ke sayarwa.”

An samu maza kusan biyar su na biyan bukatarsu da wannan yarinya.

Da manema labarai su ka tuntubi Rabi Salisu, ta ce yanzu ana kula da yarinyar sakamakon cututtukan da ta kamu da su, da kuma wasu rauni a bangaren al’aurarta.

Zuwa yanzu shugabar kungiyar ta AFN ta bayyana cewa an kama mutum hudu daga cikin wanda ake zargi, ana cigaba da bincike domin a gurfanar da su.

Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘Yan sanda na Jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige, ya ce mutane biyu daga ciki sun amsa laifinsu, sauran biyun ba su kai ga amsa laifin na su ba, sannan ana neman daya daga ciki Wanda ya tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: