Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta soke duk wani bikin babbar sallah mai zuwa.

Jawabin hakan ya fito daga bakin kwamishinan yaɗa labaran gwamna Mallam Muhammad Garba.

Gwamnatin ta soke duk wani shagali sakamakon ƙara yaɗuwar cutar corona a Najeriya.

Sai dai za a yi sallar idi bisa dokokin da gwamnatin ta saka don kaucewa tyaɗuwar cutar.

Haka zalika a jihar Jigawa ma gwamnatin jihar ta soke duk wani shagalin biki a jihar duba ga yadda ake samun ƙaruwar masu ɗauke da cutar a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: