Shugaban kasar Najeriyi yayi Allah wadai da kisan da Yan Tada kayar baya suka yiwa Ma’aikatan Agaji na Majalisar Dinkin Duniya.

Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya na bayyyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar mai dauke da sa Hannun sa.

Sannan ya kara da cewa gwamnatin najeriya bazata lamunci dukkanin yadda yan tada kayar baya ke cin karen su ba babbaka.
Don haka zasu cigaba da kokarin kakkabe yan tada Kayar baya dake Arewa maso Gabas dama Sassan najeriya.

Cikin sanarwar ya jajantawa iyalan wadanda yan Ta’addan suka hallka, tare da yabawa sojojin dake yaki da masu tada Kayar baya.

An dai ga wani faifan bidiyo a ranar Laraba, an Nuno yadda yan Ta’adda Suka kashe wasu Yan kungiyar Agaji biyar da suka Yi garkuwa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: